YADDA TIKTOK KE TUNZURA MATASAN LARABAWA SON KUDI

Kakakin TikTok ya ce an sauke manhajar sama da biliyan 2 a
duniya
Daga: sabitu umar galadima
7 Yuli 2022
Mohamed Ghadour yana shafe sa’a hudu a kullum da wayarsa
yana hada sabbin hotunan bidiyo na TikTok.
Ya ce abin ba a cewa komai, domin a duk wata yana samun
abin da ya kama daga dala 1000 zuwa 3000.
Kodayake manhajar TikTok ba ita kadai ba ce hanyar samun
kudinsa, to amma tana da muhimmanci sosai a wannan fanni
a wurinsa.
Ya ce akwai mutane da yawa da ya sani da suke samun har
kusan dala dubu 10 daga manhajar ta yada hotunan bidiyo.
Mohamed ya ce shi da sauran masu amfani da TikTok
kamarsa suna samun kudi ne ta hanyar tsarin nan na asusun
da masu manhajar ke biyan wadanda suka fi sanya hotunan
bidiyo da yawa (Creator Fund).
Inda suke hada guiwa da masu kamfanoni da ke tallata 
kayansu ko ayyukansu ta shafin.
Ya ce yi wa wani kamfani bidiyo na tallata hajarsa kan sama
mishi kusan kashi 60 cikin dari na kudin kayan a duk lokacin da
ya yi.
Duk da cewa masu bibiyar abubuwan da Mohamed ke sanyawa
yawanci suna bin shafinsa ne saboda bidiyo da yake yi na
harkokin ilimi,
kan yadda za a tallata abu ta intanet, inda yake da mabiya
sama da rabin miliyan, kowannensu yana da buri daya ne
kawai, burin kuwa shi ne yadda zai yi kudi da sauri.
Mohamed Ghadour yana da mabiya kusan rabin miliyan
Kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna yawan
mutanen da ba su da aiki a kasashen Larabawa ya kai kusan
miliyan 14.3 a 2021, kuma yawancinsu matasa ne.
Yadda ake yin wayoyi masu kyamara iri-iri da kuma manhajoji
irin su Tik Tok, wadanda za ka iya yin siddabaru da hoto iri
daban-daban, yadda  kake so, kuma ka yada su.
Wannan wata dama ce ga mutane da yawa ta yin fice da kuma
samun kudi, wadda ba za su iya bari ta wuce su ba.
A ‘yan shekarun nan aikin masu kirkirar abubuwa da kuma
tasiri a shafukan sada zumunta da muhawara sun zama wasu
fitattun ayyuka masu zaman kansu.
Wasu ‘yan kalilan din masu amfani da shafukan sada zumunta
kan samu kudade sosai fiye da yawancin masu ayyuka na yau
da kullum da aka sani.
Mai shekara 30, Mohamed, wanda dan Masar ne da ke zaune
a Saudi Arabia, sa’ana ne, to amma yana samun kusan ninki 10
na abin da nake samu a lokacin ina dan-jarida a kasashen
Larabawa.
‘’Za ka iya samun dala dubu 10 a wata daya ta hanyar Tik Tok,
idan kana so.
Ya danganta ne ga yawan mabiyanka da kuma irin bidiyon da
kake yi,’’ in ji wani fitacce a TikTok, Ismael Elabras.
Ismael – wanda inkiyarsa ita ce "Elkhal", ko "Kawu" a Larabci,
yana da mabiya kusan miliyan daya.
Yayin da Ismael mai shekara 50, dan kasar Lebanon, wanda
mai tasiri ne da fadi a ji a shafukan sada zumunta da
muhawara, yake samun kudi ta hanyar sanya hotuna a TikTok,
kamar Mohamed, to amma shi yana samun karin kudinsa ta
wata hanyar daban.
Shi Ismael, yana kuma yin bidiyo da sauran abubuwa domin
amfanin wadanda ke neman aiki da kaura zuwa wata kasa da
kuma masu neman tallafin karatu.
Ismael yana samun karin kudi daga masu kiransa su tattauna
da shi bayan sun kalli bidiyonsa, domin ya ba su shawara ko
karin bayani.
Ya ce idan ya yi haka to zai iya samun sama da albashinsa na
wata a cikin ‘yan kwanaki.
'‘Ka sayar da ilimi da kwarewar da kake da su domin samun
kudi. Abu ne na cude-ni-in-cude-ka,’’ in ji shi.
To amma fa ba kullum ake kwana a gado ba.

Comments