Lamarin rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin kudu maso gabashin kasar musamman ma a jihar Imo – Sai dai kuma a yayin da ake yawan zarginta da kai hare- hare, kungiyar IPOB ta fito ta magantu inda ta daura laifin kashe-kashen da ake fama da shi kan tawagar tsaro na Ebubeagu – A takaice dai kungiyar masu neman kafa kasar Biyafaran ta lissafo sunayen wasu mutane da ta ce sune ke haifar da karya doka a yankin da ake magana a kai Imo - Yayin da yankin kudu maso gabashin kasar ke ci gaba da fuskantar kashe-kashen mutane da sauran ayyukan ta’addanci, kungiyar aware ta masu neman kafa kasar Biyafara ta daura laifin kan wasu tawagar yan tsaro na Ebubeagu. Kungiyar ta yi zargin cewa mambobin kungiyar tsaron Ebubeagu ne ke da alhakin kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a jihar Imo da kudu maso gabashin kasar.POB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas Hoto: Nigeria Police Force Kungiyar ta kuma lissafo sunayen shugabannin da ke aiwatar...
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sunayen fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata. Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ce ta fitar da jerin sunaye na mutum 69 a ranar Juma'a, kwana uku bayan kai harin. A sakon da ta aika wa manema labarai, hukumar ta wallafa har da hotunan mutanen. Hukumar gidan yarin ta ce za a iya kallon cikakken jerin sunayen a shafinta na intanet www.corrections.gov.ng/ eccapees. A jikin hotunan mutanen da aka wallafa din duk suna sanye da inifom din gidan yarin, kuma da sunan kowa a kasan hoton. Hoton mutum 69 ne hukumar gidan yarin ta fitar, wadanda ta ce na 'yan kungiyar Boko Haram ne da wasu daurarru wadanda shari'arsu take da nasaba da ta'addanci, wadanda suka arce daga gidan kurkukun bayan 'yan bindiga sun fasa gidan. Hukumar ta jera hotunan wadanda suka tseren ne da sunayensu. Kana ta ba da wasu lambobin waya da ta ce 'yan Najeriyar za su iya tuntubarta ta layukan wayar, don sanar da jami...
Comments
Post a Comment