LAMARIN RASHIN TSARO NA CI GABA DA TA'AZZARA A YANKIN KUDU MASO GABASHIN KASAR MUSAMMAN MA A JIHAR IMO
Lamarin rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin kudu
maso gabashin kasar musamman ma a jihar Imo
– Sai dai kuma a yayin da ake yawan zarginta da kai hare-
hare, kungiyar IPOB ta fito ta magantu inda ta daura laifin
kashe-kashen da ake fama da shi kan tawagar tsaro na
Ebubeagu
– A takaice dai kungiyar masu neman kafa kasar Biyafaran
ta lissafo sunayen wasu mutane da ta ce sune ke haifar da
karya doka a yankin da ake magana a kai
Imo - Yayin da yankin kudu maso gabashin kasar ke ci gaba da
fuskantar kashe-kashen mutane da sauran ayyukan ta’addanci,
kungiyar aware ta masu neman kafa kasar Biyafara ta daura
laifin kan wasu tawagar yan tsaro na Ebubeagu.
Kungiyar ta yi zargin cewa mambobin kungiyar tsaron
Ebubeagu ne ke da alhakin kashe bayin Allah da basu ji ba
basu gani ba a jihar Imo da kudu maso gabashin kasar.POB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen
mutane a kudu maso gabas Hoto: Nigeria Police Force
Kungiyar ta kuma lissafo sunayen shugabannin da ke aiwatar
da kashe-kashen mutanen a yankin Orlu na jihar Imo a
matsayin:
1. Chibuike Igwe
2. Paul Udenwa daga Amaifeke Orlu
3. Okwudili Dim wanda aka fi sani da ‘One Nigeria’
4. Mutumin da ake kira Sky daga Umutanze Orlu
5. Mutumin da ake kira 2men daga Umuna a Orlu.
Sauran mutanen da ke addaban yankin sune:
1. Cyril Amasiatu wanda aka fi sani da wasara
2. Iron Agbaradu daga Amagu
3. Chinedu kwamandan Agbaradu-Amagu
4. Cheta odinkenma – Amagu
5. Uchenna Nwachukwu
6. Chibyke Gezek Amagu
7. Chukwudi Odimegwu
Masu yiwa mambobin ESN sojan gona a Orsu Ihiteukwa Uru
1. Mutumin da ake kira Sky
2. Mutumin da ake kira “No one”
3. Mutumin da ake kira “Double lion”
4. Mutumin da ake kira “Commander”.
A cewar kungiyar, wadannan mutane da aka ambata a sama
sune ke aikata kashe-kashen mutane a yankin.
“Wadannan mutanen da aka ambata a sama suna da
hannu a wajen aikata laifukan da ke faruwa a wadannan
garuruwa da suka hada da garkuwa da mutane, sace-
sacen motoci da sauransu. Don haka kungiyar IPOB ta
ayyana nemansu ruwa a jallo, kuma duk wanda ya bayar
da bayanai masu amfani zai samu tukwici mai tsoka.
“Wadannan miyagu da aka ambata a sama sun yiwa
mutanenmu da ke zama a yankin Orlu na jihar Imo barna
sosai. A kodayaushe IPOB na fada ma jama’a cewa
wadannan yan iska da aka ambata a sama suna daga
cikin laifukan da ke faruwa a kasarmu.
“Kada a bari wani bara-gurbi ya bata IPOB. Ya kamata a
hukunta wadannan shaidanun da masu daukar nauyinsu.”
Comments
Post a Comment