Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sunayen fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sunayen fursunonin da
suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata.
Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ce ta fitar da jerin
sunaye na mutum 69 a ranar Juma'a, kwana uku bayan kai
harin.
A sakon da ta aika wa manema labarai, hukumar ta wallafa har
da hotunan mutanen.
Hukumar gidan yarin ta ce za a iya kallon cikakken jerin
sunayen a shafinta na intanet www.corrections.gov.ng/
eccapees.
A jikin hotunan mutanen da aka wallafa din duk suna sanye da
inifom din gidan yarin, kuma da sunan kowa a kasan hoton.
Hoton mutum 69 ne hukumar gidan yarin ta fitar, wadanda ta
ce na 'yan kungiyar Boko Haram ne da wasu daurarru wadanda
shari'arsu take da nasaba da ta'addanci, wadanda suka arce
daga gidan kurkukun bayan 'yan bindiga sun fasa gidan.
Hukumar ta jera hotunan wadanda suka tseren ne da
sunayensu.
Kana ta ba da wasu lambobin waya da ta ce 'yan Najeriyar za
su iya tuntubarta ta layukan wayar, don sanar da jami'anta duk
wani bayanin da zai taimaka wajen cafke su.
Sai dai da wuya mutane su rarrabe wadanda ake zargi da
ta'addancin ta sunayen da aka wallafa, kasancewar sunaye ne
na yanka.
Alhali mafi yawan mayakan Boko Haram sun fi shahara ne da
lakabi…inda, misali za ka ji ana ce da su Abu wane da
makamantansu.
Sannan an wallafa sunan garuruwansu da yarensu da kuma
adireshinsu.
Kazalika hukumar gidan yarin ta ce za ta fitar da karin bayani a
kan sauran daurarrun da suka gudu daga kurkukun Kujen.
A ranar Talata da daddare ne wasu mahara suka afkawa gidan
yarin inda suka dinga harbe-harbe da tayar da nakiyoyi.
Tun washegarin kai harin hukumar da ke lura da gidajen-yarin
ta ce fursunoni 879 ne suka tsere.
Amma daga bisani sanarwar da mai magana da yawun gidan-
yarin, Abubakar Umar ya sanya wa hannu, ta ce wasu fursunoni
sun koma don radin kansu amma kawo yanzu ana neman
fursunoni 443.
Tun da farko Ministan Tsaron Najeriya, Bashir Magashi, ya ce
kimanin fursunoni 600 ne suka tsere a yayin harin da aka kai
gidan-yarin na Kuje.
Ministan, wanda ya tabbatar wa BBC wannan labarin, ya kara
da cewa kusan 300 daga cikinsu sun mika kansu ga hukumomi
don radin kansu yayin da jami'an tsaro suka kamo wasu daga
cikinsu.
Ministan ya dora alhakin harin kan kungiyar Boko Haram, yana
mai cewa akwai kimanin mayakan kungiyar akalla 64 a gidan-
yarin lokacin da aka kai harin.
Magashi ya kuma tabbatar da mutuwar jami'in Civil Defence
daya.
Comments
Post a Comment