Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da sunayen fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talata. Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ce ta fitar da jerin sunaye na mutum 69 a ranar Juma'a, kwana uku bayan kai harin. A sakon da ta aika wa manema labarai, hukumar ta wallafa har da hotunan mutanen. Hukumar gidan yarin ta ce za a iya kallon cikakken jerin sunayen a shafinta na intanet www.corrections.gov.ng/ eccapees. A jikin hotunan mutanen da aka wallafa din duk suna sanye da inifom din gidan yarin, kuma da sunan kowa a kasan hoton. Hoton mutum 69 ne hukumar gidan yarin ta fitar, wadanda ta ce na 'yan kungiyar Boko Haram ne da wasu daurarru wadanda shari'arsu take da nasaba da ta'addanci, wadanda suka arce daga gidan kurkukun bayan 'yan bindiga sun fasa gidan. Hukumar ta jera hotunan wadanda suka tseren ne da sunayensu. Kana ta ba da wasu lambobin waya da ta ce 'yan Najeriyar za su iya tuntubarta ta layukan wayar, don sanar da jami...