SABODA BUDURWA: FITACCEN DAN KWALLON ARSENAL YA TABBATAR DA KARBAR ADDININ MUSLUNCI
Thomas Partey ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya musulunta shi ne, yana matukar son budurwarsa ‘yar kasar Morocco Daga: sabitu umar galadima – Da yake bayar da karin bayani, dan wasan tsakiyar na Ghana ya tabbatar da cewa babu bambanci tsakanin addinan biyu – Thomas yana magana ne yayin wata tattaunawa ta yau da kullun da 'yar jaridar kafar watsa labarai Nana Aba Anamoah Ghana - A karshe dai mataimakin kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta maza ta Ghana, Black Stars, Thomas Partey, ya tabbatar da jita-jitar da ake yadawa na cewa yanzu ya Musulunta. A wata ‘yar gajeriyar hira da Nana Aba Anamoah, Thomas ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya addini ne saboda yana kaunar budurwarsa kuma babu bambanci tsakanin Kiristanci da Musulunci.A cewarsa: "Ina da yarinyar da nake so, na san 'yan matan kodimo na za su rabu da ni amma ba matsala ... Na girma tare da Musulmai don haka a karshen dai abu daya ne nakarbwi musulunci Abin da 'yan Ghana ke cewa Sorkpor Che Tsatsu yayi sharh...